KINGDOM PLANTAE
Kingdom Plantae Kingdom Plantae ya ƙunshi dukkan tsirrai waɗanda ke yin photosynthesis domin samar da abinci ta amfani da hasken rana, carbon dioxide, da ruwa. Su ne autotrophic (suna samar da abincinsu da kansu) kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da iskar oxygen a duniya. Siffofin Tsirrai a Kingdom Plantae 1. Multicellular: Duk tsirrai suna da ƙwayoyin halitta masu yawa. 2. Eukaryotic: Suna da sel mai nucleus. 3. Cell Wall: Sel ɗin tsirrai suna da bangon sel mai ƙarfi wanda aka yi da cellulose. 4. Chlorophyll: Suna da chlorophyll a cikin chloroplast wanda ke taimakawa wajen photosynthesis. 5. Non-Motile: Ba su iyayin motsi daga wuri zuwa wuri. Rarrabuwar Kingdom Plantae Ana raba tsirrai a cikin Kingdom Plantae bisa tsarin jikinsu da halayensu: 1. Bryophytes (Non-Vascular Plants) Ba su da tsarin jijiyoyi (vascular tissues) na ruwa da abinci. Suna rayuwa a wuraren da ke da ruwa sosai. Misalai: Mosses, Liverworts. 2. Pteridophytes (Seedless Vascular Plants) Suna d...